Munich: Mahara sun kashe mutane da dama | Labarai | DW | 22.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Munich: Mahara sun kashe mutane da dama

Jami'an tsaro a birnin Munich na Jamus sun ce mutane da dama sun rasu yayin wasu suka jikkata sakamakon harbi da wani dan bindiga ya yi a wani rukunin shaguna.

Wata mai magana da yawun 'yansadan Munich din ta ce ya zuwa yanzu dai ba su kai ga tantance ko maharin shi kadai ne ko kuma akwai karin wasu ba sai dai bisa ga irin bayanan da suke samu yanayi harin ya fi karfin a ce mutum guda ne ya kai shi.

Shaidun gani da ido sun ce an fara harbe-harben ne a wani gidan cin abinci da ke cikin rukunin shagunan wanda ke da kantuna da yawansu ya kai 135. An dai fara harbe-harben ne daidai lokacin da mutane ke hada-hadarsu.

Yanzu haka jami'an tsaro sun yi wa wannan waje kawanya inda suke kokarin kame maharan da kuma kubutar da mutane da ke ciki, kazalika sun kuma tsaurara matakan tsaro a sassa daban-daban na Munich din.