Muhawara tsakanin manyan ′yan takara a zaben Jamus | Labarai | DW | 01.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Muhawara tsakanin manyan 'yan takara a zaben Jamus

'Yan takaran shugabancin gwamnatin Jamus za su tafka muhawara tsakaninsu a daidai lokacin da ya rage makwani uku a gudanar da zabe.

Shugabar gwamnatin Jamus kana 'yar takarar jam'iyar CDU Angela Merkel da kuma wanda zai kalubalanceta karkashin inuwar jam'iyar SPD Peer Steinbrück za su tafka muhawara tsakaninsu a kafar telebijin a wannan Lahadin kan manufofin da suka sa a gaba. 'Yan jarida hudu ne dai za su shafe mintuna 90 suna yi musu tambayoyi a fannoni daban daban kama daga na siyasar cikin gida har i zuwa na rikicin kudin da kasashen Turai ke fama da shi, da kuma uwa uba rikicin kasar Syriya. Muhawarar dai na daga cikin abubuwan da suka fi muhummaci a yakin neman zaben shugabancin gwamnati a tarayyar Jamus. Ana sa ran cewa Steinbrück na SPD da farin jininsa ya ja baya idan aka kwatanta da Merkel ta CDU zai iya kokarin caccakar wasu manufofi na abokiyar hammayarsa, a daidai lokacin da ya rage makwanni uku a gudanar da zaben 'yan majalisa da zai bayar da damar fitar da shugaban gwamnati.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Mohammad Nasiru Awal