WasanniAfirka
Morocco ta samu tsallakawa zuwa zagaye na gaba na AFCON
December 30, 2025
Talla
A gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana da ke gudana yanzu haka a kasar Morocco, an fara shiga matakin yada kanin wani, inda mai masaukin baki Morocco ta samu nasarar tsallakawa zuwa zagaye na gaba, bayan lallasa Zambia da ci 3-0 a daren Litinin.
Haka zalika Afirka ta Kudu ma ta shiga wannan zagaye na 'yan 16, bayan doke Zimbabwe da 3-2.
Sai Mali da ta tsallake rijiya da baya wajen tsallake siradi, inda ta tashi canjaras da Comoros babu ci a tsakaninsu, wato 0-0.
Karin bayani:
Masar na sahun farko wajen shiga zagayen 'yan 16.
Najeriya wadda tuni ta shiga wannan mataki, a wannan Talata za ta yi wasanta na karshe a rukuni, inda za ta fafata da Uganda.
Sai wasa tsakanin Jamhuriyar Benin da Senegal.