WasanniTurai
Mbappé ba zai buga El-Clasico na Real Madrid da Barcelona ba
May 10, 2026
Talla
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid da ke kasar Spain, ta sanar da cewa fitaccen 'dan wasanta Kylian Mbappé, ba zai samu damar buga wasan hamayya na El-Clasico da za ta kara da babbar abokiyar gabarta Barcelona ba, a daren Lahadi.
Karin bayani: Yadda ta kaya a karshen mako cikin Labarin Wasanni
Kungiyar ta ce Kylian Mbappé, wanda kuma shi ne kyaftin din kasar Faransa, har yanzu bai kammala murmurewa daga raunin da ya samu ba, a fafatawar da suka yi da Real Betis, a ranar 24 ga Afirilun 2026.
Karin bayani: Italiya ta bijire tayin Amurka na maye Iran a kofin duniya
Wannan wasa na yau ka iya tantance kungiyar da za ta lashe La Liga, domin ko Barcelona ko da canjaras ta yi, shi ke nan ta daga kofin.