A Najeriya, yara mata Musulmi na gwagwarmaya a fannin kwallon kafa
Galibin mazauna jihar Kwara da ke Najeiya sun kasance Musulmai, inda kuma addini ya ke da tasiri a rayuwar mutane, amma yanzu an samu 'yan mata masu sha'awar kwallon kafa da suka al'adun da aka saba.

Burin kwallon kafa duk da kalubale
Lokacin da Maryam Muhammed take daura takalmin kwallo domin zuwa samun horo a makaranta da ke garin Ilorin, tana jin zafi amma ta saka hijabi saboda al'umar da take rayuwa wasu ba su yarda da sabanin haka ba. Muhammed mai shekaru 17 tana shan zolaya lokacin da take tafiya zuwa samun horon kwallon kafa a Model Queens Football Academy.
Tarbnakin al'adu da addinai
Ilorin ke zama fadar gwamnatin jihar Kwara. Duk da karuwan sha'awa na kwallon kafa tsakanin mata, sai dai akwai karancin masu shiga wasan kamar yadda Ambali Abdulrazak wani jami'in gwamnatin ya shaida wa Reuters. Saboda da dalilai na al'adu da addini kwallon mata bai samu karbuwa ba. Amma ana yunkurin samun sauyi.
Muhimmancin imani
"Sun ce ba zan samu nasara kan komai ba. Amma na yi imanin zan samu wani babban abu," a cewar Muhammed. Duk da akwai takura, yana da muhimmanci ta saka hijabi lokacin wasa maimakon guntun wando. "Wani lokaci ina ji kamar na cire hijabi, amma ba zan iya fitar da gashi na ba," ta ce. "Na saka a matsayin Musulma ta gari."
Goyon bayan iyali
Mahaifiyar Muhammed, Kehinde Muhammed, ta fuskanci suka saboda ta bar 'yar-ta tana wasan kwallon kafa. "Mutane da dama suna kashe mun kwarin gwiwa," a cewar ta, kuma tana farin ciki da lambar yabo da 'yar-ta ta samu. "Amma ina girmama ra'ayin yarana.. Ina goyon bayanta sannan ina mata addu'a." Ita ce ke dinka hijabin 'yan wasan domin ya saje da kayan wasan.
Hijabi a wasan kwallon kafa na mata
Hijabi wanda yake rufe kai da wuya, hukumar FIFA ta haramta, wadda take kula da wasan kwallon kafa na duniya, a shekara ta 2007 saboda dalilan kare lafiya, abin da ya janyo cire 'yan wasan Iran mata daga wasannin neman shiga Olympics na 2012. An sasauta hanin a shekara ta 2012 sannan aka sake amincewa da hijabi a shekara ta 2014.
Sauya tunani
MAi horas da 'yan wasan Muyhideen Abdulwahab kullum yana kara musu karfin gwiwa yana kuma kokarin sauya musu tunani. "Muna fita dmin ganawa da iyaye, a shaida musu cewa akwai dokoki na amincea da saka tufafi na kamala," a cewar sa "Duk da haka wasu suna nuna tirjiya."
Kwallon kafa na mata na smaun daukaka
Wasan na kara hakaba tsakanin 'yan Najeriya, sakamakon nasarar tawogar mata ta 'yan kwallon kafa na kasa, the Super Falcons, da kara smaun masu daukan nauyi tun daga mataki na kasa. Lig na kwallon kafa na mata na Najeriya yana daya daga cikin masu karfi na Afirka, inda kungiyoyin kudancin kasar ke jan ragama daga birane irin Lagos da Fatakwal (Port Harcourt).
Wajen haduwa kan kwalon kafa
A Najeriya wuraren haduwar jama'a suna zama na kallon kwallo tsakanin kungiyoyi. Lig na mata na kasar ya samu karuwa masu zuwa kallo da kaso 40% tun daga shekara ta 2020, sanna kuma karuwar masu kallo ta akwatin talabijin da kaso 35% a cewar wani kamfani kula da harkokin yada labarai da yake bin lamarin sau da kafa, kuma yake bin diddigin masu zuwa kallon wasa.
'Kwallon kafa shi ne burina'
Bayan shan kaye, Maryam Muhammed ta fice daga dakin kallon wasan ba tare da sanin kowa ba, inda ta koma kallon wayarta ta hannu. Irin goyon ta take samu daga iyalanta da karfin imanin da take da shi ke ba ta karfin gwiwa da nutsuwa. "Ina son wannan wasan. Ina sha'awarsa," ta ce. "Tun da iyaye suke goyon baya na, babu abin da zai tsayar da ni. Kwallon kafa shi ne burina."