Miyagun aiyuka sun karu a Jamus | Labarai | DW | 04.05.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Miyagun aiyuka sun karu a Jamus

Wani rahoton ma'aikatar cikin gidan tarayyar Jamus ya bayyana samun karin masu aiyukan batanci da kaso 08.5 cikin 100 a wannan shekara fiye da na shekarar da ta gabata.

Ministan cikin gidan Jamus Horst Seehofer da ke kaddamar da sabon rahoton a gaban manema labarai a wannan Talata, ya zargi jam'iyyar masu tsananin kyamar baki da aikata fiye da rabin ta'adin miyagun aiyukan, baya ga wadanda aka gudanar a yayin gangamin adawa da matakan yaki da corona a wasu sassan kasar.

Wannan ne dai alkaluma mafi muni da hukumomin kasar suka bijiro da su na masu aikata barna, idan aka yi la'akari da rahotannin da suka fitar a shekarun da suka wuce, lamarin da ke zame wa kasar wata babbar barazana.