Kungiyar EU na yin taro kan batun bakin haur
July 12, 2018Talla
Taron wanda shi ne za a yi a karon farko a karkashin jagorancin Austriya da ta karbi ragarmar kungyar ta EU. Zai tantance matakan da aka tsayer cikin sabani tsakanin kasashen na mayar da 'yan cirani zuwa Afirka wadanda aka ceto daga tekun Bahrum. Daga cikin ministocin har'da na Jamus Horst Seehofer wanda ya kalubalanci shugabar gwamnatrin Jamus a game da batun 'yan ci rani a rjejeniyar da suka cimma a makon jiya.