An yi kira da tsaurara dokokin mafaka a Jamus
October 1, 2015Ministan cikin gidan Jamus Thomas de Maiziere ya yi kira da a takaita yawan 'yan gudun hijira da za a karba a kasar. Ministan ya fadi hakan ne lokacin mahawara a majalisar dokoki ta Bundestag kan yi wa 'yancin samun mafakar siyasa a Jamus kwaskwarima, inda ya yi kira da a tsaurara dokokin tare kuma da gaggauta duba takardun 'yan gudun hijira.
"Daga cikin matakan da muke shirin dauka sun hada da: duk wanda ya ki komawa gida bayan an yi watsi da bukatunsa na neman mafaka, za a janye masa 'yancin samun wani tallafi da aka tanadar wa 'yan gudun hijira, in ban da muhimman abubuwa na bukatun yau da kullum."
A lokaci daya kuma gwamnatin Jamus na duba yiwuwar fadada matakan shigar da bakin cikin al'ummar kasar, musamman ma wadanda ke da kyakkyawar damar samun izinin ci gaba da zama a kasar.