Merkel ta yi gargadi bayan sassauta dokar Corona | Labarai | DW | 11.05.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta yi gargadi bayan sassauta dokar Corona

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira ga Jamusawa da su yi taka tsan-tsan da kuma ci gaba da mutunta matakin sanya tazara a tsakaninsu da kuma saka takunkumi domin kauce wa komawa gidan jiya.

Wannan na zuwa ne kwanaki kalilan bayan sassauta dokar kulle da takaita zirga-zirga bayan annobar Coronavirus ta soma ja da baya a kasar. Merkel ta yi wannan gargadi ne a karshen wani taro da ta gudanar ta bidiyo da hukumomin kiwon lafiya na kasar a wannan Litinin. Gwamnatin kasar ta Jamus ta sanar da ware kudi Euro miliyan 750 domin taimakawa ga aikin binciken samo allurar yaki da cutar ta COVID-19.

Alkalumman wannan Litinin dai sun nunar da cewa mutane kusan dubu 173 suka kamu da cutar ta COVID-19 a kasar ta Jamus inda ta halaka mutane sama da dubu bakwai da 580 a yayin da wasu dubu 143 suka warke.