Merkel ta isa inda Germanwings ya fadi | Labarai | DW | 25.03.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel ta isa inda Germanwings ya fadi

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel da takwaranta na Faransa Francois Hollande sun isa inda jirgin Germanwings ya fadi a Faransa.

Shugabannin dai sun je wajen ne don ganewa idonsu abinda ya faru daidai lokacin da kasashen Turai ke cigaba da nuna alhininsu dangane da faduwar jirgin a tsaunukan da ke kudancin Faransa, inda ake zaton fasinjojin jirgin da ma'aikatansa 150 sun rasu.

Masu bincike dai a cigaba da tattara bayanai don gano dalilin faduwar jirgin kana ana kokari wajen tataro gawarwakin mutanen da ke cikin jirgin.

A nan tarayyar Jamus ma dai ana cigaba da nuna alhini ga wanda suka rasu kana jama'a da dalibai na ta kai furanni gaban wata makaranta da ke kusa da birnin Düsseldorf wadda dalibanta 16 da malamansu biyu ke cikin wanda wannan hadari ya rutsa da su.