1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jamus ba za ta tilasta rigakafin corona ba

Abdullahi Tanko Bala
July 13, 2021

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce babu wanda zai tsira daga annobar corona har sai an yi wa kowa rigakafi musamman da bullar sabon nau'in kwayar delta mai matukar hadari.

https://p.dw.com/p/3wQkO
Deutschland | Merkel besucht Robert-Koch-Institut RKI
Hoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

Shugabar gwamnatin Jamus Angela ta jaddada cewa ana bukatar yi wa jama'a da dama rigakafin corona kafin dage dukkan matakan takunkumi da aka sanya.

Wannan ya biyo bayanin cewa Ingila za ta dage dukkan takunkumi daga mako mai zuwa.

Angela Merkel wadda ta kai ziyara cibiyar yaki da cutattuka masu yaduwa ta Robert Koch dake birnin Berlin ta ce Jamus ba ta da niyyar bin sahun Faransa da sauran kasashe wajen tilasta jama'a yin rigakafin.

"Bamu da niyyar bin salon matakin da Faransa ta dauka. Har yanzu muna matakin farko ne na gabatar da rigakafin, muna yin tanadin alluran ga dukkan mai bukatar a yi masa rigakafi."