Merkel na ziyarar bankwana a Turkiyya | Labarai | DW | 16.10.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel na ziyarar bankwana a Turkiyya

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta gana da takwaranta na Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wannan Asabar a ziyarar da ake wa kallon ta bankwana ce.

A wannan Asabar Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke kai wata ziyara kasar Turkiyya don ganawa da Shugaba Recep Tayyip Erdogan, a ziyarar da ake ganin ta bankwana ce ga Merkel da ke gab da barin madafun iko.

Burin Turkiyya na zama mamba a Kungiyar tarayyar Turai nan gaba da kuma tsarin karbar 'yan gudun hijira da 'yancin dan Adam na daga cikin batutuwan da ake sa ran shugabannin biyu za su tattauna a yayin ganawar.

Merkel dai ta taka muhimmiyar rawa a yarjejeniyar da kasashen Turai suka kulla da gwamnatin Ankara kan dakile kwararar baki 'yan gudun hijira, inda yanzu ake da sama da 'yan gudun hijira miliyan uku da Turkiyya ta tsugunar a cikin kasar.