Merkel da Trump sun gana gabannin zabe | Labarai | DW | 23.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Merkel da Trump sun gana gabannin zabe

Trump da Merkel dai sun sha gwara kai kan batutuwa kamar sauyin yanayi da 'yan gudun hijira da ya ce kuskure ne Merkel ke yi a Jamus.

A daren ranar Juma'a shugaba Donald Trump na Amirka ya kira shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta wayar tarho in da ya yi ma ta fatan alkhairi gabanin zaben gama gari da za a yi a karshen wannan mako.

A cewar fadar White House Trump ya kira shugabar ne don ma ta fata kasarta ta yi zabe lafiya ta gama lafiya. An dai ga gwaruwar kawuna tsakanin Trump da Merkel musamman kan batutuwa da suka shafi sauyin yanayi da ma batun tsarin Trump na daukar Amirkawa farko a ko me za a yi, ga bayyana tsarin Merkel na karbar 'yan gudun hijira da cewar babban kuskure ne.