MDD tayi kira daa dakatar da zartar da hukuncin kisa akan Ibrahim da Awad | Labarai | DW | 03.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

MDD tayi kira daa dakatar da zartar da hukuncin kisa akan Ibrahim da Awad

Shugabar majalisar kare hakkin jamaa ta MDD ,tayi kira ga shugaban kasar Iraki Jalal Talabani daya dakatar da zartar da hukuncin kisa akan mutane biyun da aka yanke musu hukunci tare da marigayi Sadam,wadanda kuma ake shirin ratayesu gobe da asuba.Komissionar majalisar Louise Arbour ta bayyana cewa ,dokar kasa da kasa ta amince da zartar da hukuncin kisa ne kadai,idan babu wani zabi Tace yadda ta bayyana matsayinta akan hukuncin Sadam a kwanakin baya,daidai yake dana wayanan jamiai nasa guda biyu ,watau Barzan Ibrahim dan uwan sadam da Awad Hamed al-Badar ,shugaban klotun juyin juya halin kasar,wadanda aka yankewa hukuncin kisa a ranar 5 ga watan Nuwamnban daya gabata.Adangane da hakane shugabar hukumar kare hakkin Jamaan tace,akarkashin dokar kasa da kasa Iraki zata iya bawa wadannan mutane biyu daman neman afuwa,adangane da hukuncin nasu.