Matsalar ′Yan Gudun Hijirar Sudan A Kasar Chadi | Siyasa | DW | 07.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar 'Yan Gudun Hijirar Sudan A Kasar Chadi

Har yau ana ci gaba da fama da kaka-nika-yi dangane da matsalar 'yan gudun hijirar Sudan da suka tagayyara a kasar Chadi

A yayinda a bangare guda ‚yan gudun hijirar ke cikin hali na kaka-nika-yi a daya bangaren kuma akwai kungiyoyin taimakon jinkai wadanda suka kasa samun wata takamaimiyar kafa ta kai taimakon ga mabukata. A lokacin da yake bayani a game da wannan mawuyacin hali Axel Melinon daga hukumar ‚yan gudun hijira ta MDD yayi nuni ne da cewar:

A halin yanzu haka muna sa ran karatowar damina kuma ‚yan gudun hijirar na nanata fuskantarmu da tambayoyi a game da lokacin da za a canza musu matsugunai. Amma fa ba mu san abin da za mu fada musu ba saboda ba mu da ikon taimaka musu. Wannan abin wahala ne da takaici. A dai wannan halin da ake ciki ba wani abin da zamu iya yi bisa manufa.

A hakika akwai shirye-shiryen taimakon da aka tanadar, inda aka kebe wani filin da za a iya yi wa ‚yan gudun hijirar muhalli na wucin gadi a tazarar kilomita 30 daga yankin da suka tagayyara a cikinsa yanzu haka. Mahukuntan kasar Chadi sun amince da wannan mataki, to amma fa lamarin na tattare da matsaloli masu yawa. Da farko dai wannan filin da aka tanadar ba ya da nisa da iyakar Chadi da Sudan, kuma in banda wani tafki dake yankin da wuya ake samun ruwa. Wato tilas ne a dasa bututun ruwa mai tsawon kilomita uku, ga kuma matsalar kiwon lafiya da wuraren gusar da najasa. Da zarar damina ta kama za a sha fama da zazzabin cizon sauro a wannan yanki, wanda kawo yanzu babu kowa a cikinsa. A nasa bangaren wani dan kasar Sudan mai suna Iman Osman dake tsakanin ‚yan gudun hijirar yayi korafi a game da tafiyar hawainiyar da ake samu, wacce ba shakka zata kara tsawwala matsalar nan gaba kadan. Wani abin fargaba kuma shi ne farmakin da sojojin Sudan da dakarun Larabawan Janjaweed ke kaiwa kan ‚yan gudun hijirar a ketaren iyakar Chadi. Wannan matsalar ta kara jefa jami’an taimakon jinkan cikin hali na kaka-nika-yi. Axel Melinon ya ce ‚yan gudun hijirar sun galabaita sakamakon tafiya mai nisa da suka yi da kuma yunwar dake addabarsu, inda ake dada samun yara dake fama da cututtukan nan masu nasaba da rashin abinci mai gina jiki. A dai wannan marra da ake ciki yanzun ba za ayi batu a game da wata mummunar masifa ba, amma fa muddin aka ci gaba da yi wa matsalar rikon sakainar kashi to kuwa nan gaba kadan murna zata koma ciki dangane da bala’in da zai biyo baya.