Matsalar tsaro na son ta gagari mahukuntan Najeriya
April 17, 2014Talla
Karuwar aikace-aikacen 'yan bindiga musamman na 'ya'yan kungiyar nan da ake kira Boko Haram da tashe-tashen hankula na kabilanci musamman a sassan arewacin Najeriya, alamu ne na gazawar gwamnatin kasar wajen magance tabarbarewar tsaro da ya addabi jama'a.