Tababa game da ikirarin kwace makaman Boko Haram a Kamaru | Siyasa | DW | 08.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Tababa game da ikirarin kwace makaman Boko Haram a Kamaru

Gwamnatin Kamaru ta sanar da cewar jami'an tsaronta sun kwace dimbin makamai a wasu hare-hare da suka kai kan maboyar kungiyar Boko Haram a iyakar kasar da Najeriya.

Sannu a hankali rikicin Najeriya na shafan kasar Kamaru yayinda wasu da ake zargin cewa yan kungiyar Boko Haram ne sun sace wasu baki 3 malaman addinin Kirista a arewacin kasar, wadda ake kyautata zaton an tafi da su Najeriya, al-amarin ya zo a daidai lokacin da gwamnatin Kamaru ta yi ikirarin kame wasu tarin makamai da ake kyautata zaton na kungiyar ta Boko Haram ne. Wakilin DW Moki Kindzeka ya yi tattaki zuwa arewacin kasar ta Kamaru inda binciken ya gudanar ya saba da ikirarin da gwamnatin ta Kamaru ta yi.

Batun kama makaman da gwamnatin Kamaru ta yi ikirarinsa dai, an fara jinsa ne a gidan radiyon gwamnatin kasar kamar haka:

"Gwamnan lardin arewa mai nesa ya gode wa dakarun tsaro da saurarn jami'an karamar hukumar Logone da Chari, wanda suka kama tarin makamai da albarusai, wadanda aka yi simogansu daga wata kasa izuwa ga kungiyar Boko Haram".

A cewar dakarun gwamnatin kasar ta Kamaru, dakarunta sun kama kimanin bindigogi 5400. Labarin makaman dai ya fara yaduwa ne bayan da Kamaru ta karyata jita-jita a kan 'yan kungiyar ta Boko Haram suna amfani da kasar wajan horas da mambobinta. Ministan sadarwa kana kakakin gwamnati Issa Tchiroma Bakari ya fada wa wakilin DW cewa, karbe makaman daga hannun 'yan kungiyar ta Boko Haram da gwamnatin Kamaru ta yi, ya nuna cewar kasar tana taya Najeriya yakar 'yan kungiyar.

"Wannan wata hanya ce da za ta karyata jita-jitar da ake yi a kan ana horas da 'yan tawaye a kasar Kamaru".

Yayin da gwamnatin Kamaru ta yi ikirarin ta karbe makamai da aka shirya kai wa kungiyar Boko Haram a wani kauye mai suna Gulfe wadanda aka nufa kaiwa arewacin Najeriya, wakilin DW ya yi tattaki zuwa wannan kauyen inda kusan dukka al'ummomin da ya tattauna da su sun karyata batun kama makamai a yankin kamar yadda wannan mutumin mazaunin kauyen ya shaida wa wakilin namu.

"Mun ga dai 'yan sandan kasar suna sintiri a nan duk dauke da makamai, a 'yan kwanakin nan kuma mun ga karin sojoji wadanda ke kai kawo a nan."

Ali Bashir shi ne sarkin kauyen Kekte wanda aka ce an samu makaman ya ce ya kadu da yadda gidan radiyon hukuma da jami'an gwamnatin suka yaudari jama'a, inda basaraken ya ce karya ce tsagwaro babu makaman da aka samu a kauyen.

"Dana rabu da su makaryata ne kawai. Ba gashi ni da kai mun zaga duk lungu da sako a wannan kauyen ba. Ka ga wasu makamai? Ni ne sarkin wannan garin idan da gaskiya ne da talakawa na sun fada min kuma idan da wannan al'amari gaskiya ne da an nuna makaman a gidan talabijin kuma da an sanar a gidajen radiyo. Me yasa ba a fada ba wannan ya nuna ne karara cewa gwamnatin kasar kawai ta fada ne domin gwamantin Najeriya tac e tana taya ta yakar 'yan Boko Haram, kada ku bari su yaudare ku".

A makon daya gabata ne kasar Najeriya ta bukaci hukumar tafkin Chadi da su kafa rundunar ko ta-kwana da za su yaki 'yan ta'adda, amma kasar Kamaru ta yi alkawarin ba da dakarunta idan akwai bukatar hakan.

Kawo yanzu dai wadanda ake zargin 'yan kungiyar Boko Haram ne sun sace 'yan kasar Faransa tara da 'yan Italiya biyu da kuma dan kasar Kanada daya duk kuma a kasar ta Kamaru, inda kasar ta yi alkawarin kama wadanda ke da laifin domin tabbatar da tsaron kasarta.

Mawallafi: Moki Kindzeka / Zainab Babbaji
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin