Bam ya kashe mutane da dama a Abuja | Siyasa | DW | 14.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Bam ya kashe mutane da dama a Abuja

Kusan mutane 100 sun rasu yayin da dama suka jikata bayan da wani dan kunar bakin wake ya dasa bam a tashar motar unguwar Nanya da ke gefen birnin Abuja. Tuni shugaban Jonathan ya ziyarci wadanda ke kwance a asibiti.

Kusan dukkanin manyan asibitocin birnin na Abuja na cike da gawawwaki da kuma masu rauni. Daga cikin wadanda suka rasa rayukansu a tashin bom da aka dana har da wadanda suka fito neman abinci. Bitrus da ke zaman daya a cikin masu alhinin da kuma juyayin rasuwar dan uwansa Ibrahim da ke zaman ma'aikaci a tashar motar, ya ce “ Na rasa kanina a wurin nan. Ina hanyar zuwa sai aka bugamin cewar fa bam ya tashi a Nyanya...Da na zo na duba, akwai gawar kanina a ciki.”

Da misalin karfe 6:30 na safiyar Litinin ne dan kunar bakin wake ya tuka motarsa kirar Golf zuwa tashar da ke cike da ma'aikata da sauran masu shirin fita neman abinci, sannan kuma ya ta da bam din a kan manyan motoci da ma kananan da ke cikin tashar.

Abuja Anschlag 14.04.2014

An yi asarar rayuka da dukiyoyi a Abuja

Wani jami'in da ke aiki a tashar da ya nemi sakaye sunansa ya shaida wa DW cewar “Motocinmu gaba daya gilasansu sun farfashe sun watse. Sannan kowa na ta guje-guje. Amma wadanda suke wurin sun ce sun zo bakin gareji sannan suka ta da bam din.”

Jami'an agaji na kungiyoyi daban daban sun ta aikin ceto tare da tantance masu rai da matattatun da ake ji yawansu ya tasamma daruruwa. Abbas Idris da ke zaman babban jami'in da ke kula da aikin ceton ya ce “ Duk sauran asibitocin da muka ga babu kayan aiki ,muna dauke mutane, mu kaisu inda kayan aiki ya ke.

Jonathan ya ziyarci asibitoci da Nyanya

Shi kansa shugaban kasar Goodluck Jonathan ya zagaya manyan asibitoci da kuma cibiyar da harin ya kai ga rutsawa da ita. A unguwar Asokoro da ke zaman asibiti mafi kusa da wurin harin ta cikin birnin na Abuja dai, Dr Henry Onyegbulam dake zaman babban jami'in dake kula da rayayyun da mattatun ya ce

Abuja Anschlag Rettungsdienst 14.04.2014

Jami'an agaji sun taka rawar gani a Abuja

Akwai masu rauni akalla 25 da ke bukatar kulawar gaggawa: Ma'aikatanmu na iyakacin kokarinsu, kuma mun nemi wadanda suke hutu da su yanke domin ba da nasu agajin.”

Wannan ne dai karo na shida ke nan cikin tsawon shekaru hudu da brinin na Abuja ke fuskantar harin bama- bamai a wani abun dake kara nuna alamar karfi da tasirin ayyukan ta'addancin da kasar ta Najeriya ke ikirarin yaka. To sai dai kuma sabon harin na zaman mafi hatsari da yawan asara ta rayuka ga mahukuntan da sannu a hankali dabarar ke neman karewa bisa tunkarar annobar .

Mawallafi: Ubale Musa daga Abuja
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe

Sauti da bidiyo akan labarin