Matsalar Manema Mafakar Siyasa A Nahiyar Turai | Siyasa | DW | 14.07.2004
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Matsalar Manema Mafakar Siyasa A Nahiyar Turai

An sake shiga wata sabuwar mahawara a game da karbar 'yan gudun hijira a kasashen Kungiyar Tarayyar Turai sakamakon tabargazar nan ta Cap Anamur a tekun Bahar Rum

'Yan gudun hijira a cikin jirgin ruwan Cap Anamur a gabar tekun kasar Italiya

'Yan gudun hijira a cikin jirgin ruwan "Cap Anamur" a gabar tekun kasar Italiya

Akwai kwararan dalilai a game da sukan lamirin kasashen Turai da ake yi. Domin kuwa tsaffin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai su 15 sun ajiye maganar karbar ‚yan gudun hijira, wacce aka dade ana sabani kanta, a gefe guda har ya zuwa lokacin da aka kuduri niyyar karbar sabbin kasashe a kungiyar. A sakamakon haka suka kasa cimma daidaituwa akan wata tsayayyar ka’ida bai daya tsakaninsu. Duk wanda yayi bitar lamarin zai gane cewar kowace daga cikin kasashen kungiyar su 25 a halin yanzu tana bin wata manufa ce ta radin kanta dangane da karbar ‚yan gudun hijira tare da fatali da ka’idojin da suka tsayar. Misali kowace daga cikin kasashen kungiyar akwai jerin kasashen da ta tanadar, wadanda a ganinta tana iya komar da ‚yan gudun hijirar zuwa cikinsu idan sun biyo ta kansu wajen shigowa cikinta domin neman mafakar siyasa. Wannan maganar tana mai yin nuni ne da yadda kasashen ke kame-kame ba tare da sun nemo ainifin bakin zaren warware matsalar ‚yan gudun hijirar ba. Duka-duka yunkuri suke yi na tace manema mafakar tattalin arziki daga dimbim masu neman mafakar siyasa dake tuttudowa zuwa nahiyar Turai. Kazalika a karkashin kudurin da suka tsayar duk mai neman mafakar siyasa wajibi ne ya gabatar da takardunsa a kasar kungiyar ta farko da ya saka kafafuwansa a harabarta wanda ke ma’anar karba-karba ko kuma kakkabe kasa daga alhakinta na ba da mafakar siyasa. A halin yanzu haka kasashen sun shigence gabar tekun Giralter domin hana tuttudowar makauratan dake barin kasashensu bisa dalilai na talauci da rashin sanin tabbas a game da makomarsu. Ainifin dalilin da ya sanya aka samu raguwar manema mafakar siyasar shi ne kwanciyar hankalin da aka samu a yankunan kasashen kudu-maso-gabacin Turai, wadanda suka sha fama da rikici a zamanin baya. Bugu da kari kuma kasashe da dama na gabacin Turai na sa ran shigowa inuwar Kungiyar Tarayyar Turai ta yadda al’ummominsu ke fata nan gaba kadan zasu samu kyautatuwar rayuwarsu. Amma a inda take kasa tana dabo shi ne kasashen Afurka da na Asiya ba su da irin wannan gata. Abu daya da zai taimaka shi ne gabatar da kwararan matakan taimakon raya kasa masu tasiri. To sai dai kuma duk da makudan kudin da aka tanadar, amma ma’amallar taimakon ba ta tafiya salin alin daidai yadda ya kamata. Wajibi ne a dauki nagartattun matakai wajen kyautata wannan ma’amalla da kuma karya alkadarin ‚yan baranda dake fasakwabrin haramtattun baki zuwa kasashen Turai, a maimakon yunkurin killace iyakokin nahiyar baki daya. Wani kuma abin da ya wajaba a ba da la’akari da shi shi ne nagartattun matakan hana wanzuwar yake-yaken dake haddasa wannan masifa ta ‚yan gudun hijirar dake watangaririya tsakanin yankunan da lamarin ya shafa ba tare da sanin tabbas game da makomar rayuwarsu ba.