1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Matatakin diflomasiyar Jamus kan Koriya ta Arewa

Gazali Abdou Tasawa
November 30, 2017

Kasar Jamus ta dauki matakin rage jami'an diflomasiyarta a Koriya ta Arewa bayan da a jiya Laraba ta gudanar da wani sabon gwajin makami mai linzami.

https://p.dw.com/p/2oZYO
Heiko Maas und Sigmar Gabriel
Hoto: picture-alliance/dpa/O. Dietze

 Ministan harakokin wajen kasar ta Jamus Sigmar Gabriel ne ya bayyana hakan lokacin wata ganawa da takwaransa na Amirka Rex Tillerson a wannan Alhamis a birnin Washigton inda yake gudanar da wata ziyarar aiki inda ya ce Jamus ta maido jami'an diflomasiyarta biyu zuwa gida kana tana shirin maido da na uku da ma daukar wasu sabbin matakan nan zuwa gaba tare da sauran kasashen Turai. 

Minista Sigmar Gabriel ya kara da cewa Jamus ta kuma ta bukaci Koriya ta Arewar da ta takaice adadin jami'an diflomasiyarta da ke a birnin Berlin. Wannan mataki na zuwa ne kwana daya bayan da Amirka ta yi kira ga kasashen duniya da su katse huldar kasuwanci da ta diflomasiyya da Koriya ta Arewar a wani mataki na tilasta mata yin watsi da shirinta na nukiliya.