Masu gini sun tono bom a Jamus | Labarai | DW | 15.11.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu gini sun tono bom a Jamus

Kimanin mutane 7,500 hukumomin Jamus suka kwashe daga gidajensu a birnin Berlin a kokarin da suka yi na lalata wani bom da aka gano a karkashin kasa da aka ajiye shi tun zamanin yakin duniya na biyu.

Bom din mai nauyin kilo 250 wasu injiniyoyi ne masu gina gidaje suka fara tono shi a unguwar Kreuzberg da ke Berlin. A ranar Asabar bayan da 'yan sanda suka kammala aikin lalata bom din sun dora hotansa a Twitter suna masu kira da jama'a cewa kowa ya koma gidansa an yi nasarar lalata shi.


Kwashe mutane irin wannan ba wani sabon abu bane a nan Jamus, domin a lokuta daban-daban an sha kwashe mutane da zarar magina suka ci karo da bom da ke kunshe a cikin kasa.