1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Jamus kan tura sojojin Amirka zuwa Afghanistan

Widerwal Rupert YB
August 23, 2017

Bayan da kasar Amirka ta sake jaddada shirinta na tura dakaru zuwa Afghanistan a kokarinta na kawar da mayakan Taliban. Kasashe kawayen Amirka sun tofa albarkacin bakinsu a ciki har' da Jamus.

https://p.dw.com/p/2ii23
USA Fort Myer Trump Rede Afghanistan Strategie
Hoto: picture-alliance/Pool via CNP/MediaPunch/M. Wilson

Ko da ya ke shugabar gwamnatin Jamus ba ta yi wani dogon jawabi ba kan shirin na Amirka, yayin da ta ke yin wata tattaunawa da wata mujallar sojan Jamus Bundeswehr, ta yi kalaman da ke zama abin jujuyawa a zukata, watau su dai suna matsayarsu, kuma shirye suke su ba da tasu gudunmawa kan yaki da ta'addanci tsakanin kasa da kasa. Shi kuwa Trump ya bayyana cewar yana da kwarin gwiwa na ganin daga wannan lokaci su kai farmaki ga makiyansu su kawar da IS su murkushe Al Qaida da taka birki ga Taliban mai kokarin kwace Afghanistan.

''Za mu tambayi kawayenmu na kungiyar NATO da sauran kawayenmu na sauran sassa na duniya su tallafa wa sabon yunkurinmu da karin soja da kudade, muna da karfin gwiwa za su yi.''

Südkorea Raketenabwehrsystem PAC-3
Hoto: picture-alliance/dpa/APLee Jin-Man

Ministar tsaron Jamus Ursula von der Leyen  ta jam'iyyar CDU jam'iyyar shugabar gwamnatin Jamus, a ranar Talata a yayin ziyararta a  sansanin ba da horon sojan ruwa a arewacin Jamus  ta bayyana cewar matakin da Amirka ta dauka na kara yawan sojanta a Afghanistan da cewa abu ne mai kyau, inda ta ce dama tuni Berlin ta kara yawan nata sojan, yayin da wasu kasashe suka janye nasu, ta ce hakan ya yi kyau da Amirka ta zo da mataki da ya sabawa na lokutan yakin neman zabe da Trump ke cewar ba za su ba da karin soja ba.