Martanin duniya dangane da shekaru biyar na 9/11 | Labarai | DW | 11.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin duniya dangane da shekaru biyar na 9/11

Kasashen duniya dake da sabanin raayi kann harkokin tarzoma,na taya Amurka juyayin wannan rana ta 11 ga watan satumba,a inda kawayenta ,suka dada lasan takobin yaki da ayyukatan taaddanci,a yayinda a hannu guda kuma yan tarzoman ke cigaba da yin Allah wadan yadda Amurka da gaza cimma komai,kana dayin alkaswrin cigaba da kalubalantar shirinta na yakansu.Dakarun Amurkan dana Philipine dake yakqan sojojin sakai a kudancin Asia dai ,sunyi adduar zaman lafiya a duniya baki daya.Ayayinda a hannu guda kuma aka gudanar adduoin cika shekaru biyar na wannan rana a kasashe Japan da Australia da Finland da koriya ta kudu da Thailand da kuma Indonesia.Jaridun Islamabad a kasar Pakistan ayau din dai,sun gavbatar da sharhuna daban daban akan harin kunar bakin waken na Amurka,sai dai mafi yawa daga cikinsu sun soki tsarin Amurka na yaki da ayyukan tarzoma,inda akanyi amfani da karfin soji,kuma hakan bazai maganta komai ba.

 • Kwanan wata 11.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu5V
 • Kwanan wata 11.09.2006
 • Mawallafi Zainab A Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu5V