1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

MINUSMA na fuskantar radadin dakatar da Jamus

Mahamadou Kane Maila(ZUD/LMJ)
August 15, 2022

Gwamnatin sojin Mali ta dakatar da aikin rundunar sojojin Jamus ta Bundeswehr daga rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato MINUSMA, lamarin da ke haifar da fargaba a game da yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/4FYxz
Außenministerin Baerbock besucht Mali
Hoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Tawagar sojojin na Jamus karkashin jagorancin kawancen dakarun Tarayyar Turai "EUTEM" ta kwashe shekaru kusan 10 a kasar ta Mali tare da MINUSMA, tana bayar da gudunmawa wajen ganin an samar da zaman lafiya. Majalisar sojojin kasar ta Mali ta bukaci rundunar Jamus din ta fice daga MINUSMA, biyo bayan korar jami'an tsaron Barkhane da Takouba na kasar Faransa. Ko wane irin tasiri, ficewar sojojin Jamus daga Mali ka iya yi ga rundunar ta MINUSMA? Abdoulaye Guindo na yin nazari kan al'amuran yau da kullum a Malin ya ce hakan tamkar wani koma baya ne ga bayar da tallafin abinci da hakar sufuri da sojojin Jamus ke taimaka wa mutanen yankin Gao da su. 

Wasu daga cikin sojojin Jamus da ke Mali
Wasu daga cikin sojojin Jamus da ke MaliHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Kimanin jami'an tsaro dubu daya da 350 na kasar Jamus ne ke a fagen dagar. Bakary Traore manazarci a fannin tsaro ne. Ya nuna fargaba a kan rundunar MINUSMA ba tare da sojojin Jamusba. Sai dai Traore ya ce sojojin Mali na son dandana karfin ikon da suke da shi ne a fagen diflomasiyya.

Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a wata ziyara da ta kai Mali
Ministar harkokin wajen Jamus Annalena Baerbock a wata ziyara da ta kai Mali Hoto: Florian Gaertner/photothek/picture alliance

A cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen Malin, Abdoulaye Diop ya fitar ya ce za a dawo da tsarin karba-karba na jami'an MINUSMA da hukumomin kasar suka dakatar a ranar 14 ga watan Yulin da ya gabata. Babban jami'in diflomasiyyar ya ce kasarsa za ta ci gaba da bin dokoki yadda ya kamata.