1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta hana sojojin Jamus fita daga kasar

July 15, 2022

Jami'an kasar Malin sun dakatar da sojojin Jamus din hawa jirgin saman da aka tsara zai tashi da su a ranar Alhamis, sakamakon rashin gabatar da wasu takardu, lamarin da Jamus ke kallo a matsayin ''cin-fuska''.

https://p.dw.com/p/4EChf
Mali | Übergangspräsident Assimi Goïta
Hoto: Präsidentschaft der Republik Mali

Hukumomin kasar Mali sun hana sojojin Jamus takwas ficewa daga kasar da ke Yammacin Afirka. Wannan na zuwa ne 'yan kwanaki bayan gwamnatin mulkin sojan Malin ta kama sojoji kusan 50 na kasar Côte d'Ivoire wadanda ta ce sun isa kasar ba tare da izini ba.

A ranar Alhamis, gwamnatin Malin ta dakatar da tsarin karba-karba na kewayawa da sojojin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da aka fi sani da MINUSMA na dan wani lokaci.