Mai yunkurin kai hari a Jamus ya kashe kansa | Labarai | DW | 13.10.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Mai yunkurin kai hari a Jamus ya kashe kansa

Mutumin nan dan kasar Siriya da ake zargi da shirin kai hari a filin tashi da saukar jiragen sama a Jamus an same shi a mace inda ake tsare da shi a birnin Leipzig kamar yadda mahukunta suka bayyana a daren jiya Laraba.

Sebastian Gemkow, ministan shari'a daga jihar Saxony da ke a Gabashin Jamus ya ce zai bada karin bayani kan dalilan da ya sa wannan matashi mai shekaru 22  Jaber al-Bakr ya kashe kansa. Ministan ya ce zai yi jawabi a taron manema labarai da misalin karfe sha daya agogon Jamus tara agogon GMT a wannan rana ta Alhamis.

Wata majiya dai da ta tsegunta wa kamfanin dillancin labaran Jamus DPA, ta ce an gano mutumin da aka tsare ya rataye kansa.

Al-Bakr wanda masu aikin bincike suka bayyana da cewa ya na da alaka da kungiyar nan ta IS an cafke shi a ranar Litinin bayan da aka dauki kwanaki biyu ana fafutikar neman inda ya boye, bayan da aka gano ababen fashewa da kayan hada su a dakin da yake zama a birnin Chemnitz.