Macron zai gana da takwarorinsa na Turai | Labarai | DW | 07.06.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Macron zai gana da takwarorinsa na Turai

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ce za yi wata tattaunawa ta musamman da shugabannin Jamus da Birtaniya da Italiya kan harajin da Amirka ta sanya kasashen Turai da ke shigar karafa Amirka.

Macron ya ce za su yi wannan zama ne gabannin taron G7 na kasashen nan masu arzikin masana'antu a duniya wanda za a yi a Kanada, inda ya kara da cewar Shugaban Kungiyar Tarayyar Turai EU Donald Tusk zai kasance a wajen zaman da za a yi. Shugaban na Faransa ya ce ya yanke hukuncin tattaunawa da takwarorin nasa ne domin daukar mataki na bai daya kan Amirka a matsayin martani kan takunkumin da ta saka musu wanda ya kaisu ga fara zaman doya da manja.