1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mace bakar fata ta farko a majalisar Jamus

Mouhamadou Awal Balarabe
October 26, 2021

Sabbin 'yan majalisar dokokin Jamus da aka zaba a watan Satumba sun kama aiki a Bundestag. Sai dai an samu sauyi fiye da shekarun baya, inda aka samu bakar fata ta farko mai suna Awet Tesfaiesus a matsayin 'yar majalisa.

https://p.dw.com/p/42C7r
Awet Tesfaiesus | Bundestagsabgeordnete Bündnis90/DieGrünen
Hoto: Yvonne Sophie Thöne

Awet Tesfaiesus lauya ce da ke da tushe da Iritiriya, wacce ta shiga harkokin siyasar Jamus tun kafin ta tsaya takara a zaben 'yan majalisar dokokin kasar. Tana fatan amfani da damar da ta samu wajen karfafa gwiwar mata da ke cin rani a kasar da su bi sahunta. Awet Tesfaiesus na aiki ba dare ba rana tun lokacin babban zaben da ya ba ta damar shiga cikin kundin tarihin Jamus na kasancewa mace ta farko bakar fata a Bundestag. Duk da cewa ta shafe shekaru tana taba siyasa a jihar da take da zama, amma wani kisan gilla na wariyar launin fata da aka yi a can ne ya girgiza ta sosai, har ya kai ta ga tsayawa takara.

Awet Tesfaiesus ta ce "Ban san dai me dalili ba, amma harin ta'addancin da aka kai a Hanau ya kai ni makura. Ina tsammanin wannan abu ya yi tasiri sosai. Sai na ji cewa ba zan iya sake jure wannan ba." 

Deutschland Hanau | Gedenken an die Opfer des Attentat in Hanau
Kashe baki da aka yi a Hanau ya yi tasiri a rayuwar Awet TesfaiesusHoto: Michael Probst/AP/picture alliance

 An kashe mutane 10 a wannan harin ta'addancin na Hanau na jihar Hessen da ke tsakiyar Jamus- inda tara daga cikinsu 'yan ci-rani ne, ko kuma iyayensu suka zo daga kasashen waje. A wancan lokaci Awet Tesfaiesus ta yi tunanin barin Jamus, saboda ta yi amannar cewa kasar ba wuri ne mai aminci ga ita da danginta ba. Amma ta sauya tunani daga baya saboda "da kamar wuya a sami kasar da ba a da wariyar launin fata a cikinta. Don haka zabi na gaba ya kasance zama a Jamus don yakar wariya launin fata."

 

Tesfaiesus na da burin kawo daidaita tsakanin jinsuna 

A mazabarta da ke wani kauye na jihar Hessen dai, ganin wata mace bakar fata a jerin sunayen 'yan takara a zabe ya zama wani sabon abu. Amma kuma burin samar da sauyi ya karin karfafa gwiwar Awet Tesfaiesus 'yar shekaru 47 da haihuwa. Amma yayin da ake ci gaba da samun jinsi dabam dabam a cikin al'ummar Jamus, yunkurin da ake yi na surka ma'aikatan cibiyoyin gwamnati da wasu jinsuna na tafiyar hawainiya. 

Majalisar dokoki ta Bundestag ga misali na da mambobi 736. amma 83 daga cikinsu ne kawai suke da asali da wata kasa ta waje. Hasali ma dai, kashi 26% na Jamusawa suna da asalin da wata kasa ta dabam. Amma a cikin Bundestag, kusan kashi 11 na 'yan majalisa ne kawai ke da tushe da wata kasa. Kasa da rabin 'yan majalisar mata ne, Kuma kafin a zabi Tesfaiesus a matsayin 'yar majalisa, ba a sami wata bakar fata a cikinsu ba.

 

Deutschland Awet Tesfaiesus
Awet Tesfaiesus na son a kafa dokar daidaita dama tsakanin 'yan JamusHoto: Privat

 Tesfaiesus na fatan zama abar koyi a Bundestag
A yanzu daga karamar mazabarta, Tesfaiesus ta zarce kai tsaye zuwa tsakiyar Berlin hedkwatar gwamnatin jamus. Amma ta zaku ta ga komai ya kankama domin ta kawo sauyi. Ta ce "Ba shakka fatana shi ne, mu ci gaba da mai da hankali kan batun bayar da damammaki daidai wa daida. Mu rinka wayar da kan jama'a,  amma kuma mu kawo sauyi ta fuskar doka"

Sabuwar 'yar majalisa Awet Tesfaiesus na da bururruka daa ta sa a gaba, amma na farko daga cikin su, shi ne yi wa wasu hidima a matsayin abar koyi da ba ta taba samu ba a Jamus.