1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran: Jamus ta bukaci kwantar da hankula

Gazali Abdou Tasawa
June 10, 2019

Ministan harkokin wajen Jamus Heiko Maas ya tattauna da takwaransa na Iran Javad Zarif a birnin Tehran a wani mataki na kwantar da hankula a yankin tekun Fasha

https://p.dw.com/p/3K8jH
Iran Die Außenminister Maas und Sarif
Hoto: picture alliance/dpa/M. Fischer

Kasar Iran ta yi kashedi ga Amirka kan rikicin kasuwancin da ta ke yi da ita. Da yake jawabi a gaban 'yan jarida a lokacin ganawarsa da takwaransa Haiko Maas na kasar Jamus da ya kai ziyarar aiki a kasar ta Iran, ministan harkokin wajen Iran din Mohammad Javad Sarif ya gargadi Amirka ta fahimci cewa ita kanta ba ta samun zaman lafiya matsawar al'ummar Iran za ta ci gaba da zama a cikin halin kunci a sakamakon takukumin tattalin arzikin kasar Amirka

"Ya ce a game da tayin tattaunawar da Amirka ke yi mana za mu karbi tayin ne idan har matakin nasu ya wuce fatar baki kawai. Kuma babban misali da za ta nuna shi ne na janye haramtaccen takukumin da ta saka mana da ya saka al'ummarmu a cikin halin ha'ula'i" 

Ministan harkokin wajen Jamus na ziyara ne a kasar ta iran da nufin shawo kanta ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da kasashen duniya a shekara ta 2015, inda ko baya ga ministan harakokin wajen zai kuma gana da shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.