1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Binciken gawa don gano dalilin mutuwa

Ramatu Garba Baba
November 2, 2018

A Najeriya da Nijar gudanar da binciken na (autopsy) abu ne da jama’a ba su yadda da shi ba duk da cewa ma gudanar da wannan bincike na bukatar kwararru masu binciken gawa.

https://p.dw.com/p/37ak7
Japan Sterben Zuhause
Hoto: Reuters/Kim Kyung-Hoon

Shirin ya duba batun binciken gawa, binciken da aka fi gudanarwa da zarar an tabbatar mutum ya riga ya mutu kuma ana son sanin dalilin ajalinsa, duk da cewa wannan batu ba sabon abu bane a kasashen da aka ci gaba amma a kasashe masu tasowa musanman wasu kasashen nahiyar Afirka kamar Najeriya da Nijar gudanar da binciken na (autopsy) abu ne da jama'a ba su yadda da shi ba duk da cewa ma gudanar da wannan bincike na bukatar kwarraru masu binciken gawa, ga kuma kudin da ake bukata wajen gudanar da binciken in har ta kama iyalan mamatan sun nemi yin binciken.

Binciken gawa don gano dalilin mutuwa

Shirin ya yada zango a jahar Kadunan Najeriya inda wakilinmu Ibrahima Yakubu ya tattauna da Dakta Maryam Abubakar  shugabar asibitin Fatima da ke unguwar Dosa a jahar Kadunan, ko me ake nufi da binciken gawa ko Autopsy a Turancin Ingilishi sai a a latsa kan shirin da ake iya saurara.