Kwanton bauna ya hallaka sojojin Najeriya a Borno | Labarai | DW | 27.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kwanton bauna ya hallaka sojojin Najeriya a Borno

Wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun hallaka sojoji guda tara na Najeriya da farar hulla guda daga cikin tawagar da ta je domin duba yiwuwar fitar da man fetir a yankin Arewa maso gabashin kasar.

Nigeria Soldaten in Damboa (Getty Images/AFP/S. Heunis)

Sojojin Najeriya da ke yakar 'yan Boko Haram

Sanarwar ta rundunar sojojin Najeriya ta ce an yi wa ma'aikatan na kamfanin mai na Najeriya na NNPC kwanton baunar ne yayin da suke dawowa daga rangadin da suka kai a cikin yankin Magumeri da ke jihar Borno.

Mai magana da yawun rundunar sojojin Sani Usman Kuka Sheka,  ya ce an samu kubutar da dukannin ma'aikatan kamfanin man, sannan gawar wani babban soja da sauran wasu gawarwakin na wasu sojojin da ta wani farar hula guda duk an samu karbo su inda aka kai su ya zuwa gidajen asibitoci.

Da farko dai an yi zaton mayakan na Boko Haram sun sace ma'aikata 10 ne masu binciken kasa na jami'ar Maiduguri, sai dai labarin da sojojin suka bayar ya nunar cewa mayakan na Boko Haram sun yi kwaton bauna ne abin da ya janyo fafatawa tsakanin su da sojojin na Najeriya da ke rakiyar wadannan masana.