Kurdawa na samun nasara kan mayakan IS | Labarai | DW | 19.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kurdawa na samun nasara kan mayakan IS

Ana ci gaba da fafatawa kan samu iko da garin Kobani na kasar Siriya, inda Kurdawa ke samun nasara a kan 'yan IS a kasar Syriya.

Mayakan Kurdawa sun samu nasarar korar 'yan kungiyar IS daga mafi yawan yankunan Kubani na kasar Siriya.

Rahotannin sun nunar da cewa ruwan wuta da dakarun Amirka ke jagoranta kan 'yan kungiyar ta IS ya taimaka wa dakarun na Kurdawa. An kwashe makwanni ana wannan fafatawa da tsagerun kungiyar ta IS wadanda ke ikirarin neman kafa daular Islama. Amma duk da ruwan wutar tsagerun na IS sun ki janyewa baki daya.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe