Kungiyar EU ta sanya takunkumi ga masu hannu a shirin juyin mulki a Burundi | Labarai | DW | 02.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kungiyar EU ta sanya takunkumi ga masu hannu a shirin juyin mulki a Burundi

A cewar mujallar kungiyar ta EU Janar Ngendakumana na daga cikin masu yin karantsaye ga yunkurin sulhunta rikicin siyasa a kasar.

Burundi Armee General Leonard Ngendakumana

Janar Leonard Ngendakumana

Daya daga cikin tsaffin dakarun soji da ya rike mukamin Janar da ya mara baya a shirin juyin mulkin shugaba Pierre Nkurunziza da ya gaza nasara a kasar Burundi a watan Mayu da ya gabata, kungiyar EU ta sanya masa takunkumi, adaidai lokacin da a ke lalubar hanyoyi na dakile rikici a kasar da ke a Gabashin Afirka.

Janar Leonard Ngendakumana na daga cikin manyan mutane hudu na kasar, da kungiyar EU ta haramta musu shiga daukacin kasashenta 28. Sannan duk abin da suka mallaka na ajiya a bankunan kasashen basu da ikon ta'ammali da su.

A cewar mujallar kungiyar ta EU Janar Ngendakumana na daga cikin masu yin karantsaye ga yunkurin sulhunta rikicin siyasa a kasar sannan yana daga cikin wadanda suka tallafa wajen tada rikici da ma kai hare-hare ta hanyar amfani da makaman gurneti.