Koyar da tarihin mulkin mallaka a Afirka | BATUTUWA | DW | 15.10.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

BATUTUWA

Koyar da tarihin mulkin mallaka a Afirka

'Yan Afirka da dama na cewar lokaci ya yi da za a koyar da tarihin nahiyar ga yara 'yan makaranta, musamman ma dai tarihi kan irin yadda aka yi wa nahiyar mulkin mallaka a shekarun baya.

Namibia Geschichte Deutsch-Südwestafrika Gefangene Hereros

Lokaci ya yi da za a fara koyar da tarihin mulkin mallaka a makarantun Afirka

Da dama dai na ganin gaza karantar da dalibai irin tarihin kasashensu na wancan lokaci, na taimakawa wajen boye ainihin abin da ya faru a lokacin Turawan mulkin mallakar. Akwai tababa mai yawa da ake ci gaba da yi game da batutuwa na tarihi da suka dangaci kasashen Afirka, musamman ma daga lokacin da Turawa suka shiga nahiyar zuwa lokacin da wasunsu suka samu mulkin kansu.

Karin Bayani: Chadi: Shekaru 60 na 'yanci daga Faransa 

Masana tarihi da sauran marubuta da dama a nahiyar, na ganin tarihin da aka bayar ya kan takaita ne ga lokacin da kasashen suka samu 'yancin kansu. Siyanda Mohutsiwa wadda marubuciya ce a kasar Botswana, na daga cikin wadanda ke da wannan ra'ayin, inda ta ke cewa hakan ne ma ya sanya take bin wasu hanyoyi na sanin tarihin kasar, sai dai ko da wannan din ma ba ta samu yadda take so ba. A hannu guda kuma, wasu masana tarihi na yin korafi kan yadda ake jirkita labaran abubuwan da suka faru a baya.

Deutsch-Südwestafrika Zeichnung Hererokrieg Hereroaufstand

Dubban al'ummar Afirka ne suka rasa rayukansu a lokacin mulkin mallakar Turawa

Galibin irin wadannan abubuwa da aka bayar da labarinsu cikin darussa na tarihi, kan kasance ba hakikanin abin da ke  kasa ba inji Faith Odele da ke zaman wata masaniyar tarihi a Najeriya. A cewarta, wannan ne ma ya sanya take ganin ya zama wajibi ga al'ummar kasar da sauran kasashen Afirka, su zabura wajen sanin tarihinsu domin hakan ne hanya guda daga cikin hanyoyin da za ta kaisu ga nasara.

Karin Bayani: Ko kasashe rainon Faransa na da 'yanci?

Wannan yanayi da ake ciki ne dai ya sanya Faith da ma sauran masana tarihi a kasashen Afirka, yin kira ga hukumomi kan su tashi haikan wajen ganin matasa sun san tarihin, ta hanyar sanya shi cikin manhajar karatu domin gudun kada su taso ba tare da sanin tarihin asalinsu ba.

Karin Bayani: Burkina Faso: Shekaru 60 da samun 'yanci

Irin wannan kira ne ya sanya hukumomi a kasar Kenya daukar matakin sanya tarihi cikin manhajar karatu a kasar, kuma tuni ma shiri ya yi nisa wajen daukar irin tsarin hukumar nan ta UNESCO ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da sha'anin ilimi ta samar. Shi dai wannan tsari na UNESCO wanda masana tarihi kimanin 230 suka yi aiki a kansa, ya himmatu ne wajen yin gyara kan yadda ake bayar da tarihi a nahiyar Afirka ga al'ummarta, musamman ma ta wannan zamanin.

 

DW.COM

Sauti da bidiyo akan labarin