Rusa mutum-mutumin ′yan mulkin mallaka | Zamantakewa | DW | 14.07.2020
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Rusa mutum-mutumin 'yan mulkin mallaka

Kisan Ba'amirken nan bakar fata George Floyd a hannun 'yan sandan Amirkan sakamakon azabtarwa, ya tayar da gyambo na wariyar launin fata da Turawan mulkin mallaka suka yi a kasashen Afirka.

BG Statuen Proteste weltweit gegen Rassismus und Kolonialismus Bristol Edward Colston (picture-alliance/NurPhoto/G. Spadafora)

Masu zanga-zangar #BlackLivesMatter# sun tumbuke tare da jefa mutum-mutumin jagoran cinikin bayi, Edward Colston cikin ruwa a Birtaniya.

Kasashen biyu dai sun fara wannan muhawarar ta share babin mulkin mallakar ko fara karantar da dalibai tarihinsa a makarantun kasashensu, bayan da wasu 'yan Afirka suka fara rusa mutum-mutumin Turawan mulkin mallakar.

A wani wurin shakatawa a babban birnin Kenya wato Nairobi wanda tsakiyarsa ke kewaye da furanni da kuma karamin bango, inda wani rubutu ke nuna cewar a baya, akwai mutum-mutumin Sarauniya Victoria ta Ingila, kaka ga Sarauniya Elizabeth ta yanzu, amma yanzu haka an rushe shi kuma an wofantar da mutum-tumunin a cikin ciyawa, kamar yadda wani dan kenya da ya ziyarci wurin shakatawar ya nuna: "Wannan mutum-mutumi ya tunatar da ni irin yadda Turawan mulkin mallaka suka wahalar da magabatanmu. Wadannan kayan tarihin suna tuna mana mummunan abin da ya faru a baya, saboda haka dole ne a lalata su a duk duniya."

Queen Victoria (imago images/Design Pics)

Sarauniya Victoria ta Ingila

A lokacin da Kenya ta sami 'yancin kanta daga Biritaniya a 1963, kasar cike take da mutum-mutumi na tsofaffin sarakunan mulkin mallaka. Sannu a hankali ne aka rusa su gaba daya, in ban da mutum-mutumin Sarauniya Victoria da ya dauki lokaci mai tsawo, har zuwa lokacin da wasu mutane da ba a san su wanene ba, suka lalata shi shekaru biyar din da suka gabata.

A Kinshasa babban birnin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ma dai, har yau mutum-mutumin Sarki Leopold na Beljiyam na dashe a gidan adana kayan tarihi na kasar. Abin da daraktan gidan José Batekele ya ce: "Gunkin Leopold na biyu yana bayyana wani nau'i na tarihi a garemu. Abin tuni ga zuri'armu. Tarihi dai ko mai kyau ko mara kyau ba a canja masa suna."

Sai dai wani babin tarihi ya nunar da cewa Sarki Leopold na biyu, ya musgunawa 'yan Kwango fiye da yadda ake zato. Ya dauki kasar a matsayin wani bangare na kadarorinsa, inda ya ke wadata kansa da arzikin albarkatun kasa da Allah ya huwace mata. Leopold dai bai san jinkai a Kwango ba lokacin da aka yi wa kasar mulkin mallaka, in ji tsohon shugaban rumbun ajiyar kayan tarihi na Kinshasa Antoine Lumenganeso: "Idan mutane ba su tattara roba da sauri ba, ana azabtar da su. An ta yanke hannayensu, har da yara. Shi ya sa suka yi magana game da jar roba."

Belgien König Leopold II Denkmal in Kinshasa Archiv 2005 (picture alliance/AP Photo)

Mutum-mutumin Sarki Leopold na Beljiyam

Shekaru da dama bayan samun 'yancin kai, lokacin da dan mulkin kama karya Mobutu Sese Seko ya hau kan kujerar mulki, ya cire dukkan gumaka ko mutum-mutumin, domin a juya babin mulkin mallaka, kuma ya canja wa Kwango suna zuwa Zaire. Sai dai bayan da aka dawo da bara bana, Zaire ta sake komawa Kawngo, an sake gina mutum-mutumin Sarkin Leopold a daura da na wadanda suka gano Kwango wato Henry Morton Stanley da David Livingstone. Amma har yanzu mutum-mutumin na ci gaba da janyo muhawara game da yadda ya kamata a yi mu'amala da tarihin mulkin mallaka a Kwangon.

Abin da ya kamata 'yan Kwango su tambayi kansu shi ne ya aka yi bakar wahala da suka sha lokacin  mulkin mallaka ba ta zame musu darasi ba, domin har yanzu kasar na fama da rikicin siyasa da na kabilanci shekaru 60 bayan samun 'yancin kai. Hasali ma a maimakon Turawan mulkin mallakar, yanzu haka sojoji suna kwace albarkatun kasa da tsoratar da jama'a. Dadin dadawa ma dai rikice-rikicen na kwango sun zame jiki, har ya sa duniya na yin buris da su, in ji wani kwararre a kasar Jason Stearns a cikin wani jawabi da ya yi a farkon wannan shekarar. n A fili yake cewa shekaru 60 bayan samun 'yancin kai, al'ummar Kwango ba sa fuskantar zalunci daga fararen fatar, amma an yi watsi da su.