1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kotu ta ja wa matakin EU na ciwo bashi birki

March 26, 2021

Kotun tsarin mulki ta Jamus ta sanar da umurtar shugaban kasa Frank-Walter Steinmeier da ka da ya rattaba hannun a kan kudurin karbo rancen kudi domin farfado da tattalin arzikin kasashen Kungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/3rFht
Bundesverfassungsgericht in Karlsruhe
Hoto: picture-alliance/dpa/U. Deck


Wannan matakin kotun tsarin mulkin Jamus na zuwa ne bayan 'yan majalisar dokokin kasar ta Bundestag suka amince da kudurin kafa asusun tallafin Turai da gagarumin rinjaye. Sai dai kotun ta ce akwai bukatar a dakatar da yunkurin domin shugabannin jam'iyyar AFD da ke da tsattsauran ra'ayi sun shigar da kara don adawa da yunkurin.
 
Tun a shekarar da ta gabata ne kasashen Kungiyar Tarayyar Turai suka amince su karbo bashin Euro biliyan 750 don farfado da tattalin arzikin kasashensu bayan da corona ya yi masa illa. Ana sa ran rarraba wa kasashen wadannan kudade daga bisani kuma su biya a hankali.

Sai dai alamu na nuna cewa kotun tsarin mulkin Jamus na bukatar akalla watanni uku kafin ta kammala nazarin ko za ta amince  shugaban kasar Jamus ya sanya hannu a kan kudurin ko kuma a'a, a yayin da kungiyar Tarayyar Turai ke jiran amincewar Jamus, a matsayinta na memba kuma kasa mafi karfin tattalin arziki  a nahiyar.