Kokarin yin sulhu a rikicin Ukraine | Labarai | DW | 29.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin yin sulhu a rikicin Ukraine

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya sanarda sabon yunkurin tattaunawar tsagaita wuta tsakanin gwamnati da 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha.

Wannan sanarwa ta Poroshenko dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ministocin kungiyar Tarayyar Turai wato EU suka yanke shawarar kara tsaurara takunkumi a kan 'yan awaren da ma Rasha da suke zargi da iza wutar rikicin na Ukraine. Poroshenko ya shaidawa taron kungiyar tuntubar juna a kan rikicin Ukraine cewa za su tattauna nan take tare da gaggauta tsagaita wuta da kuma dakatar da amfani da manyan makamai a tsakaninsu da 'yan awaren. Ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Belarus ta sanar da cewa kungiyar tuntubar junan za ta gudanar da taro a wannan Jumma'a a birnin Minsk, kuma shugabannin 'yan awaren gabashin Ukraine din sun amince cewa su ma za su halarci taron.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba