Kokarin warware rikicin PDP a Najeriya | Siyasa | DW | 18.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kokarin warware rikicin PDP a Najeriya

Kwamitin tsare tsaren jam'iyyar PDP mai mulki na ci gaba da kai ziyara sassan Najeriya, a yunkurinta na gano bakin zaren warware rikicin cikin gida ta ya yi mata katutu.

Jam'iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta dukufa ka'in da na'in wajen dinke barakar cikin gida dake addabar jam'iyyar a kusan dukkan jihohin da take mulki, shi yasa ma shugaban jam'yyar yake zagayawa jihohin domin yin sulhu.

Tawagar shugabannin Jamiyyar PDP da ta hada da shugaban jamiyyar ta kai ziyara yankunan kudu maso gabas da kudu maso kudancin Najeriya, a wani mataki na son dinke baraka da sasanta juna a jam'iyyar ta PDP. Sai dai bisa wasu al'amura da suka bayyana, da alamu akwai sauran rina a kaba ga jamiyyar ta PDP mai mulki, dangane da bukatar jam'iyyar na son hada kawunan 'ya'yanta, musamman a yankin Niger delta.

Tawagar da ta hada da kusan daukacin kwamitin tsare tsare na jam'iyya, da kuma ke karkashin jagorancin shugaban jamiyyar ta PDP ta kasa wato Alhaji Bamanga Tukur ta fara kai ziyararta ne a kudu maso gabashin na Najeriya, wato shiyyar da kabilar Igbo take. Kuma bayanai sun nunar da cewar, ko da yake wasu gaggan yan jam'iyyar yankin kamar su Ike Ekweramodu ba su halarci taron da akai ba, kwamitin na tsare tsare ya sadu da 'yan jam'iyyar da dama kuma zaman da akai, ya nuna an fahimci yunkurin uwar jam'iyya na son dinke baraka da sasanta juna da kuma bukatar gwamnatocin jahohin yankin na su bujuro da ayyuka na raya kasa.

Daga yankin kudancin Najeriyar dai, magabatan PDP sun kuma ziyarci jihar Bauchi, inda suka gana da 'yan jam'iyyar dake yankin arewa maso gabashin Najeriyar, duk a matakin ganin cewar an gano bakin zaren warware matsalar cikin gida daya jima yana ciwa jam'iyyar tuwo a kwarya.

Mawallafi : Mohammad Bello
Edita : Zainab Mohammed Abubakar

Sauti da bidiyo akan labarin