Kokarin murkushe 'yan jarida a Turkiya
February 27, 2017Talla
Jaridar Die Welt ta Jamus wadda a nan ne Yucel kewa aiki yayin da 'yan sanda suka cafke shi a Turkiyan, ta tabbatar da gurfanar tasa a gaban kuliya. Yucel dai na rike da fasfo biyu na kasashen Jamus da Turkiya, kuma yana zaman dan jaridar Jamus na farko da jami'an 'yan sandan na Turkiya suka tsare a wani bangare na kokarin murkushe 'yan jaridu da kasar ke yi, tun bayan da mahukuntanta suka sanya dokar ta baci sakamakon yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba da ta fuskanata a shekarar da ta gabata ta 2016.