Kokarin kula da ′yan gudun hijira | Labarai | DW | 03.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kokarin kula da 'yan gudun hijira

Mambobin kungiyar Tarayyar Turai EU sun amince da bayar da kimanin biliyan uku na kudin euro domin tallafawa 'yan gudun hijira a Turkiya.

'Yan gudun hijira da ke kaura zuwa Turai

Miliyoyin 'yan gudun hijira ne a 'yan shekarun nan suka yi kaura zuwa Turai

Wannan makudan kudaden dai za a yi amfani da su ne domin inganta rayuwar 'yan gudun hijirar da ke zaune a Turkiya, wanda a cewarsu za su taimaka wajen rage tururuwar da suke yi wajen shigowa nahiyar Turai ko ta halin kaka domin samun ingantacciyar rayuwa. Nahiyar Turai dai na fama da matsalar kwararar 'yan gudun hijira da ke neman mafaka wadanda aka kiyasta cewa sama da miliyan guda ne suka ketara zuwa Turan. Da damansu dai sun kauracewa yakin da ake fama da shi ne a Siriya.