1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Hadin gwiwar yakar tarzoma a Sahel

August 25, 2022

Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso sun bayyana aniyar karfafa huldarsu a fannin tsaro domin kare iyakokinsu daga yawan hare-haren 'yan ta'adda.

https://p.dw.com/p/4G33h
Benin | Fotoreportage Marco Simoncelli aus Porga
Hoto: Marco Simoncelli/DW

Sanarwar kasashen biyu wanda suka ratabawa hannu a ranar Litinin din da ta gabata dai ta bukataci da takworarsu ta Mali ta dawo a cikin G5 Sahel duba da yadda yankin Sahel ke fama da hare-haren 'yan ta'adda.

A karshen watan Mayun da ya gabata a karkashin jagorancin majalisar sojojin milkin kasar Mali ta fice daga kawancen G5 Sahel mai kunshe da kasashe biyar a nahiyar Afrika yankin sahel din, da hujjar an hana su jagoranci karba-karba na kawancan a yayinda kamun ludayin ya kawo a gare su. saidai a cewar masana irin su Bakary Sambe mai sharhi a kan tsaron yankin sahel kana daraktan makarantar Think-Tank Afrika dake Timbuktu wannan babban kuskurene kasar Mali ta yi.

"Ficewar kasar Mali daga kawancen kasashen G5 Sahel bayada wani muhimmanci, tunda kasar Mali ta kasance cibiyar wannan matsalar tsaro inda dalilin ta kasar Niger da Burkina Faso lamarin tsaro ya shafe su. don haka ina tunanin dawowa a G5 Sahel ga Mali yanada kayu, muna ganin yadda kungiyoyin EIGS masu ikkirarin Jihadi suka mamaye yankunan (Menaka da Gao), kuma mun gani yadda ta kasance a yankin tessit kusa da Gao a kwanakin baya.  karfafa hulda ta kasashen musamman tare da Nijar a halin yanzu abu ne mai kyau".

A halin yanzu dai kasar Mali ta zama saniyar ware a yankin sahel a fagen kulla kawancen yaki da ta'addanci tun bayan ficewar ta daga G5 sahela a farkon wannan shekarar. Boukari Salif Traore jami'i ne a cibiyar Afrilog masannin tsaro da bunkasar yankin sahel  yana mai ra'ayin cewa kawancen G5 Sahel bashi aiki da dokokin da ya  shinfida a yayin kadamarda ayukan G5 Sahel.

"G5 Sahel an assasata ne a tan tsarin kasar Mali a shekarar 2014, sai a 2017 kafin ta soma aiki ta da dakaran sojin hadin kai na mambobin ta , amma ba'a tba aiki da bukatun a ka shimfida a yayin kaddamar da ayukan gadan-gadan, wata matsala kuma da suke fama da ita shine na samun asalin ta daga Shugabanin kasasahe biyar manbobin ta, dalilin haka a ke zargin wasu daga cikin shugabanin suna hana  dakaransu gudanarda aikin su yadda ya kamata a fagen tabbatarda tsaro domin cimma borin su".

G5 Sahel ta kunshi kasashe biyar da suka hada da  Mali da Chadi, da Murtaniya da Burkina Faso da kuma Nijar. Mambobin wannan kawance bayan kasar Murtaniya da Chadi hare-haren yan ta'adda ya  haifarda dubban yan gudun hijira a wasu sansankasar.