1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen EU na yunkurin dakile tashin hankali a Bangui

December 20, 2013

Faransa ta nemi takwarorinta na Turai da su dafa mata wajen ganin ta kashe wutar rikicin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wanda ya ke ci gaba ruruwa

https://p.dw.com/p/1AdnB
Francois Hollande da dakarun kasarsa da ke aiki a Jamhuriyar Afirka ta TsakiyaHoto: picture-alliance/AP

Shugaban Faransa Francois Holland ya ambata hakan ne a jiya Alhamis, jim kadan bayan kammala taro na ranar farko da shugabannin kungiyar Tarayyar Turai ke gudanarwa a birnin Brussel na kasar Belgiyum, inda ya ce ya na fatan kasar Poland za ta fidda sanarawa a wannan Juma'ar ta cewar za ta aike da dakarunta don dafawa takwarorinsu na Faransa da sauran kasashen Afrika.

Shugaban na Faransa ya ce da zarar Poland din ta yi hakan to ya na da yakinin cewar sauran kasashe za su biyo baya, wanda hakan zai nuna cewar aikin wanzar da zaman lafiyar da za a yi a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiyar ya zama na hadin gwiwa tsakanin kasahen kungyiar EU da takwarorinsu na Afrika wanda zai share fagen sama musu tallafi, sai dai guda daga cikin jakadun EU din da ya zabi a sakaya sunansa ya ce samun tallafi don aiwatar da wannan aiki ka iya daukar makonni masu yawa ko ma watanni domin kasashen Turai ne ba EU ba suka rungumo aikin.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman