Kasashen duniya sun kira taro kan Burundi | Labarai | DW | 12.11.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashen duniya sun kira taro kan Burundi

Majalissar Dinkin Duniya da Kungiyoyin AU da EU sun kira zuwa ga shirya wani taron gaggawa tsakanin bangarorin kasar Burundi masu gaba da juna domin shawo kan rikicin ta hanyar lumana

Kasashen duniya sun yi kiran gwamnatin kasar Burundi da wakillan 'yan adawar kasar zuwa ga shirya wani taron gaggawa domin shawo kan rikicin kasar ta hanyar lumana.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Shugabannin kungiyoyi uku da suka dada da MDD da kungiyoyin EU da na AU suka fitar dabra da taron koli na kasar Malta, sun ce sun cimma matsaya kan shirya wannan taron gaggawa tsakanin bangarorin da ke hamayya a kasar ta Burundi a birnin Adis Ababa ko kuma na Kampala a karkashin jagorancin Shugaban kasar Uganda Yoweri Museveni.

Kungiyoyin sun bayyana damuwarsu ainun da sabon salon da rikicin kasar ta Burundi ya dauka a baya bayan nan a sakamakon soma aikin neman karbe makamai da karfi daga hannun masu adawa da milkin Shugaba Pierre Nkurunziza.

MDD ta ce ta fara nazarin yiwuwar aikawa da sojojinta daga jamhuriyar demokradiyyar Kwango zuwa kasar ta Burundi idan dai har rikicin ya ki ci ya ki cinyewa.