Kasashe za su kashe biliyoyi kan Siriya | Labarai | DW | 04.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe za su kashe biliyoyi kan Siriya

Jamus za ta bada gudummowar sama da Euro biliyan biyu kana Birtaniya da Norway Euro biliyan 2.6 domin tallafawa 'yan gudun hijirara Siriya da ke gudun hijira a sassan duniya.


Shugabannin gwamantoci da jami'an diplomasiyya daga kasashe 70 sun yi alkawarin bayar da tallafi kwatankwacin biliyoyin daloli ga miliyoyin 'yan kasar Siriya da suka rasa matsugunensu. Sakamakon yakin kasar na tsawon shekaru biyar dai , miliyoyin 'yan kasar ne ke ci gaba da kwararar zuwa Turai domin neman mafaka. Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya ce halin da kasar ta Siriya ke ciki, ba abunda za'a lamunta ba ne.

Babu mafitar da za'a cimma ta hanyar amfani da bakin bindiga. Hanya daya itace tattaunawa a siyasance da diplomasiyya, wanda hakan ne kadai zai tsame al'ummar Siriya daga irin wadi na tsaka mai wuya da suke ciki, inji Ki-moon

A taron bada tallafi ga 'yan Siriyar da ke gudana a birnin London a wannan Alhamis, Sarki Abdullah na Jordan ya ce kasarsa ba ta da sukunin kulawa da 'yan gudun hijirar Siriya miliyan 1.3 da ke kasar. Jamus da ke zama mai masaukin 'yan gudun hijira sama da miliyan guda, ta yi alkawarin bada gudunmowar Euro biliyan 2.3 ga kungiyoyin agaji na kasa da kasa da ke tallafawa 'yan gudun hijirar Siriya.

Daga cikin wannan adadi a cewar shugabar gwamnati Angela Merkel, za'a bayar da kimanin Euro biliyan 1.2 a wannan shekarar. Tuni Britaniya da Norway suka yi alkawarin kashe kwatankwacin Euro miliyan 2.6 nan da shekara ta 2020. Kasashen uku da Kuwaiti ne dai suka shirya wannan taron agaji zagaye na hudu, domin tallafawa 'yan gudun hijira sama da miliyan 10 daga kasashen Iraki da Siriya.