London shi ne birnin na biyu mafi girma a Turai kuma shi ne babban birnin kasar Burtaniya. Birnin na da yawan mutane kimanin miliyan takwas da rabi.
Hada-hadar kasuwanci na daga cikin abubuwan da aka san birnin London da shi baya ga kasancewa da ya yi birni mai cike da kayan tarihi. A London din ne fadar gidan sarautar Ingila take. Birnin ya yi fice ta bangaren jiragen karkashi kasa wanda ake da su tun sama da shekaru 100 da suka gabata.