Kasashe na taya Merkel murna kan zaben Jamus | Labarai | DW | 25.09.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kasashe na taya Merkel murna kan zaben Jamus

Cikin 'yan gaba-gaba wajen mika sakon taya murna ga shugabar gwamnatin ta Jamus na zama kawayen kasar ta Jamus daga nahiyar Turai kamar Faransa.

Al'ummomin kasa da kasa na ci gaba da martani game da sakamakon zaben gama gari da aka kammala a ranar Lahadi, sakamakon da zai ba wa Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel dama ta dorawa a karo na hudu na mulki a kasar.

Cikin 'yan gaba-gaba wajen mika sakon taya murna ga shugabar gwamnatin ta Jamus na zama kawayen kasar ta Jamus daga nahiyar Turai kamar Faransa inda tuni Shugaba Emmanuel Macron ya ce ya kira shugabar gwamnatin ta Jamus ya tayata murna ya kuma sake jaddada mata cewa suna hade wajen aiwatar da abubuwan da za su bunkasa kasashensu. Haka shi ma Firaminista Mariano Rajoy na kasar Spain, shima Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bi sauran shugabanni wajen taya Merkel murna.