Kasashe 7 masu karfin tattalin arziki suna taro a Jamus | Siyasa | DW | 07.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kasashe 7 masu karfin tattalin arziki suna taro a Jamus

Manyan kasashe duniya da suka fi ci gaban masana'anzu suna cia gaba da tattauna al'amuran duniya a taron kolin da suke yi a garin Elmau na kudancin Jamus.

Firaministan kasar Ingila David Cameron ya yi kira ga shugabannin kasashen Turai da su hada kai domin ci gaba da hukunta kasar Rasha duk kuwa da iri-irin matsalolin da hakan ke janyo wa wasu kasashen na Turai. Cameron ya yi wadannan kalammai ne a ranar lahadi lokacin da aka fara taron kasashe bakwai masu karfin tattalinn arziki a duniya da ke gudana a Kudancin nan Jamus. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ita ce mai masaukin baki da suka hada har da shugabannin Japan da Italiya da Kanada da Faransa

Tu da farko dai Shugaban kasar Amirka Barack Obama da ke halartar wannan zaman taro na kwanaki biyu, ya ce wannan taro zai bada damar duma batun rawar da kasar Rasha ke takawa a rikicin gabashin Ukraine inda ya ce 'yan awaren gabashin kasar masu goyon bayan Rasha ke fafatawa da dakarun gwamnatin kasar.

Taron ana yinsa ne duk da zanga-zanga mai tsanani da mahalartansa suke fuskanta daga kungiyoyi dabam dabam, tun daga na kare hakkin 'yan Adam har ya zuwa wadanda suke ganin shi kansa taron bata kudi ne kawai da ya kamata a yi amfani dashi domin kyautata jin dadin rayuwar wadanda ke zaune cikin wahala a yankunan duniya dabam dabam. Daga baya ranar Litinin, shugabannin wasu kasashe, cikinsu har da Muhammadu Buhari na Najeriya za su tattauna da takwarorinsu na manyan kasashen 7 masu karfin tattalin arziki.

Sauti da bidiyo akan labarin