1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Erdogan ya shirya hadewa da EU

Abdul-raheem Hassan MAB
January 12, 2021

Shugaban Recep Tayyip Erdogan ya ce Turkiyya a shirye take ta maida huldar diflomasiyya da Kungiyar Tarayyar Turai, tare da neman hadin kan kasashe 27 na kungiyar domin fahimtar juna.

https://p.dw.com/p/3nplw
Türkei | Satellitenstart | Türksat 5A
Hoto: Murat Kula/AA/picture alliance

Yayin da yake jawabi ga jakadan EU a birnin Ankara, Erdogan ya bayyana fatan bude sabon babi na kawo karshen takaddama tsakanin Turkiyya da Girka bayan kwarkwaryar zaman sulhu tsakanin kasashen biyu.

Sai dai a loakci guda shugaban na Turkiyya ya kuma gargadi Girka da ta iya takunta a duk wani matakin da zai haddasa tashin hankali.

A shekarar 2015 Turkiyya ta fara tattauna yarjejeniyar shiga Kungiyar Tarayyar Turai, sai dai lamarin ya ci tura, bayan da EU ta zargi gwamnatin Ankara da yi wa tsarin dimukaradiyya karan tsaye.