Kara hada gwiwar Jamus da Faransa a Afirka | Siyasa | DW | 21.01.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Kara hada gwiwar Jamus da Faransa a Afirka

Ministar tsaron Jamus, Ursula von der Leyen ta gana da takwaran aikinta na Faransa Jean Yves Le Drian domin tattauna manufofinsu na dakatar da rikice-rikicen a Afrika.

Faransa, tsohuwar uwargijiyar kasashen Afika da dama, yanzu haka tana da sojojinta 1600 dake taimakawa rundunar kasashen Afrika dake da sojoji 4000 a cikinta a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. A watan Disamba na bara, shugaban gwamnatin Jamus, Angela Merkel tace ba zata amince da tura sojojin kasar zuwa aiyukan tabbatar da zaman lafiya a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya ba kamar yadda Faransa ta dade tana bukata. Duk da haka, ministan harkokin wajen Jamus, Frank Walter Steinmeier ya yabi kwazon da Faransa take yi a Jamhuriyar ta Tsakiyar Afirka, inda yace mu Turawa ya kamata a matsayinmu na makwabtan Afirka, mu nuna godiya ga iin kokarin da Faransa take yi domin hana aukuwar kazamin abu a nahiyar.

A Jamhuriyar Afrika Ta Tsakiya, ana ci gaba da mummunan yakin basasa tsakanin Kiristoci da Musulmi, tun bayan juyin mulki da Musumi yan tawaye suka yi a shekara ta 2013. Fiye da rabin yan kasar miliyan biyar a yanzu sun dogara ne ga taimakon jin kai daga ketare, yayin da majalisar dinkin duniya tayi gargadi game da yiwuwar samun kisan kare dangi, idan har kasashen duniya basu fadada kokarinsu na hana aukuwar hakan ba.

Karkashin wani shiri da aka yi, sojojin kungiyar hadin kan Turai tsakanin 500 zuwa 1000 ne zasu kara karfafa matsayin rundunar kasashen Afirka a Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya. To amma Jamus tace ba zata tura sojojinta dauke da makamai zuwa kasar ba. Ministan harkokin waje Steinmeier da kakakin gamnatin Steffen Seibert duka sun sanar da cewar Jamus bata da sha'awar tura sojojin nata zuwa can. Duk da haka, kakakin jam'iyyar SPD a fannin tsaro, Rainer Arnold, ya soki wannan matsayi na gwamnati inda yace:

Duk wanda yake da burin ganin an sami ci gaba a game da manufofin tabbatar da tsaron nahiyar Turai baki daya, to kuwa bai kamata ya kyale Faransa tayi komai ita kadai ba tare da an taimaketa ba.

A daura da haka, ministan tsaro, Ursula von der Leyen tace Jamus din zata iya bayar da taimakon suhuri da magunguna da ma'aikatan jiyya. Tace wadannan fannoni ne da ake bukatarsu, kuma muke iya bada gudummuwa ba tare da kace-nace ba. Sai dai ya zuwa yanzu babu wanda ya nuna alamar yana bukatar irin taimakon da Jamus tace zata iya bayarwa.

Faransa a watan Janairu na shekara ta 2013 ta taimaka aka dakatar da aiyukan kungiyoyin yan tawaye a Mali. Tun bayan wannan lokaci sojoji 170 na Jamus suke kasar, inda suke horad da sojojin rundunar kasar ta Mali da kuma taimakawa aiyukan rundunar kiyaye zaman lafiya ta majalisar dinkin duniya da Afirka, wato MINUSMA a takaice. Roderich Kiesewetter, kakakin harkokin waje na jam'iyyar CDU ya nunar da cear:

A Mali ana iya ganin cewar tsoma bakin kungiyar hadin kan Turai ta taimaka dawo da zaman lafiya a kasar. Yanzu kuma abin da ake magana shine mu taimakawa kokarin da Faransa take yi ta amfani da wasu fannoni na kungiyar hadin kan Turai.

Jamus dai tana iya yanke kudiri a game da irin wannan taimako tun a mako mai zuwa, idan majalisar dokoki tazo muhawara kan yiwuwar kara wa'adin kasancewar sojojin kasar a Mali da zai kare a karshen watan Fabrairu.

Mawallafi: Sven Pöhle/Umaru Aliyu
Edita: Saleh Umar Saleh

Sauti da bidiyo akan labarin