Kananan yara na fama da yunwa a Borno | Labarai | DW | 19.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Kananan yara na fama da yunwa a Borno

Hukumar kula da kananan yara ta UNICEF, ta yi gargadin cewa akalla yara 49,000 na fama da yunwa na rashin abinci mai gida jiki a jihohin da suka sha fama da rikicin Boko Haram a Najeriya.

Hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta yi gargadin cewa akalla yara 49,000 da ke yankin arewa maso gabashin Najeriya na cikin barazanar rasa rayukansu sakamakon rashin abinci mai gina jiki.

A cikin watan Juni da ya gabata wata kungiyar agaji ta fidda wani rahoto da ke cewa mutanen da suka tsere daga rikicin Boko Haram, na mutuwa a dalilin rashin wadataccen abinci. A yanzu dai Hukumar ta UNICEF na kira ga kungiyoyin agaji na kasa da kasa da su gaggauta kai dauki a jihohin Arewa maso Gabashin Najeriya wadan da suka sha fama da rikicin Boko Haram musamman ma Jihar Borno dan ceto rayuwar yara kanana da ke cikin garari na rashin abinci mai gina jiki.